fbpx
Thursday, August 11
Shadow

An gano maboyar da ‘yan Bindiga ke gasa naman mutane suna ci

Jami’an rudunar tsaro ta farin kaya, ta DSS ta gano wasu sansanoni da ake kashe tare da gasa gawarwakin mutane domin ci a cikin jihohin Imo da Anambra.

An ga kawunan mutane a yanke kuma a warwatse a sansanonin masu garkuwa da mutane a jihar.

Tuni dai hukumar ta kama wasu wadanda ake zargi da hannu cikin miyagun ayyuka da ba su yi kama da na bil adama ba.

Tawagar jami’an tsaro ta hadin gwiwa ce ta kai samamen ba zata a sansanonin masu garkuwa da mutane a jihohin Imo da Anambra; inda suka riske gawarwakin mutane a yashe, wasu a bushe a sa’ilin da wasu daga cikinsu kuwa an gasa su wanda ake zargin mutanen da ke garkuwa da bil’adaman kan ci.

Wannan yunƙuri dai ya kai ga kama masu garkuwa da mutane sama da 30 a waɗannan sansanoni.

Daraktan hukumar DSS a jihar Imo, Wilcox Idaminabo, ya ce: “Rundunar tsaro ce ta hadin gwiwa da ta hada da sojoji, ‘yan sanda da kuma DSS suka gudanar da wannan aiki.

“Mun kai farmaki ga maboyar masu garkuwa da mutane a wata unguwa a jihar Anambra da kuma Orsu a jihar Imo.

“Al’umma sun yi gudun hijira, babu wanda ke zaune a wurin. Yaran sun mallakarwa kansu wani sansani mai yawa kuma wannan wani lamari na tayar da ƙayar baya ne. Babu wanda ke zaune a wurin.

“A yayin da ake gudanar da wannan samamen ne, jami’an tsaro suka samu nasarar ceto Eze Acho.

Wannan samamen da jami’an hadin gwiwa suka gudanar a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo da kuma Uli da ke karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra, ya yi sanadin kama mutum sama da30 da ake zargi sun mayar da sassan jikin bil’adama abincinsu.

Kuma a wurin ne jami’an suka kubutar da Eze Acho Ndukwe na al’ummar Ihube a karamar hukumar Okigwe ta jihar Imo, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar Lahadi.

“Ina mamakin, a cikin karni na 21, mun lura cewa har yanzu mutane suna cin naman mutane a nan. Mun ga naman mutum a gashe.

“Mun ga gawarwaki da yawa. Abin da suke yi shi ne garkuwa da kashe wasu daga cikin mutanen.

“Hakika, sun yi musayar wuta da jami’an tsaro, amma mun rinjaye su kuma muka kama da yawa daga cikinsu,” kamar yadda ya ce.

Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma ya ce gaskiya ta yi halinta cewa wadanda ke aikata miyagun ayyuka kamar waɗannan su ne annobar wannan yankin Igbo a kudu maso gabashin Najeriya.

Ina so in yaba wa jami’an tsaro a jihar Imo da suka hada kawunansu tare da tabbatar da cewa akalla mutanen Imo sun dawo gida su yi bukukuwan Kirsimati.

Lamari ne na matukar nuna damuwa da mamakin yadda daukacin karamar hukuma kamar ta Orsu za a yi watsi da ita har ta fada a hannun masu masu cin naman mutane. Daga abin da muka gani yanzu za ku yarda da ni cewa wadannan miyagun mutane ne da basu da wata makoma ta alheri da suke shirya-wa kansu. Ta ya zasu gasa kuma su ci naman bil’adama in ba dabbobi masu cin naman mutane ba?

Ta yaya kuma za mu bi da irin wadannan wawaye idan ba doka ta yi aikinta ba ba?

Cin naman mutane har yanzu a wasu kasashen duniya na a wannan zamani, duk da cewa galibin al’ummomi suna ɗaukarsa abin ƙyama.

Duk da haka, akwai wuraren da cin naman ɗan adam ya kasance tamkar wani bangare na al’ada.

Mutane suna komawa cin naman mutane saboda wasu dalilai, kama daga bukukuwan addini zuwa matsananciyar bukata ta abin duniya da dai sauransu.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.