fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

An Gano ‘Yar Gidan Tukur S. Tukur (Dandugaji) Da Ta Bace jiya

A jiyane Tsoho taurron fina-finan Hausa na barkwanci Tukur S. Tukur wanda aka fi sani da dandugaji ya bayyana cewa Diyarshi ta bata bayan data tafi makarantar Islmaiya aka nemeta aka rasa, to jarumin ya fitar da sanarwar cewa Allah ya bayyana diyar tashi tun a jiyan da misalin karfe hudu na yamma kuma ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka bayar da gudummuwa wajan gano diyar tashi Shukra.

Ga sakon da fitar kamar haka:
“ALHAMDULILLAH  ALHAMDULILLAH. DA MISALIN KARFE 4:00 PM, NA SAMI KIRAN WAYA DAGA GIDAN RADIO FREEDOM CEWAR AN GA SHUKRATA.
“TO INA MIKA DIMBIN GODIYA GA JAMA’A DA SUKA TAYA NI DA ADDU’A, DA MASU ‘COMMENT’ DA ‘SHARE’ DA ‘LIKE’, ALLAH YA SAKA MUKU DA ALHERI, ALLAH YA YAYE MANA MATSALOLIN MU.
“INA KARA MIKA GODIYA TA GA RADIO FREEDOM DA AMINCI RADIO, DA XPRESS RADIO DA SAURAN GIDAJEN RADIO DA SUKA BADA SANARWA. ALLAH SAKAWA KOWA DA ALKHAIRI DA MASU KIRAN WAYA DA WADANDA SUKA ZO GIDA DAN JAJANTA MANA.
ALLAH BA MU LAFIYA DA ZAMA LAFIYA”.
Muna fatan Allah ya kiyayae na gaba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  Za a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin Najeriya - Nimet ...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *