fbpx
Sunday, August 7
Shadow

An gargadi Bola Tinubu kan daukar Shettima ko Zulum a matsayin abokin takararsa

Yayin da yanzu makonni biyu kacal suka rage da hukumar zabe tacewa ‘yan takara su bayyana abokan takararsu, Tinubu har yanzu bai bauyana nasa ba.

Amma bayan ya gama bincike an samu labari daga majiya mar karfi cewa Tinubu yace gwamna Zulum na Borno ko kuma Kashim Shettima zai zaba.

Amma dan takarar PDP, Atiku da tsohon hadimin Goodluck, Omokri sun gargadi Tinubu cewa kar ya zabi daya daga mutanen da yake shirin dauka.

Inda sukace masa shi Kashim Shettima ya kasa kare daliban Chibok a lokacin da aka yi garkuwa dasu, yayin da kuma suka ce masa shima Zulum baya kaunar kirista.

Leave a Reply

Your email address will not be published.