Rahotanni daga kasar Mali na cewa an garzaya da tsohon shugaban kasar da Sojoji suka hambarar a juyin Mulki, Ibrahim Boubacar Keita zuwa kasar UAE dan neman Lafiya.
Keita ya samu rakiyar Matarsa, Amina sa wasu likitoci da jami’an tsro. Kamfanin dillancin labaran AP ya bayyana cewa da yammavin Yau, Asabar ne aka tafi da tsohon shugaban zuwa UAE.
A baya dai mun ji cewa an garzaya da tsohon shugaban kasar Asibiti a Mali bayan da ciwon mutuwar barin jiki ta kamashi.
A wani Labari me dangantaka da wannan kuma Rahotanni daga kasar na cewa sojojin masar 2 ne aka kashe a wani hari.