An yi Jana’izar Kwamandan Soja, Kanal DC Bako da Boko Haram suka kashe a harin kwantan Bauna da duk suka kaiwa tawargarsa.
A wajan jana’izar, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana marigayin a matsayin gwarzon soja wanda ya rike rundunarsa dake kula da Damboa wanda yace a karkashinsa ba’a taba samun nasara akan Garin ba.
Gwamna Zulum yace an sanar dashi cewa marigayin bashi da gidan kansa da haka yawa iyalan nasa kyautar gida, za’a gina musu.
Sannan kuma ya ji hukumar soji tace ta dauki nauyin karatun ‘ya’yansa dan haka gwamnatin jihar Borno zata taimakawa hakan inda yawa iyalan alkawarin Miliyan 20 wanda yace daga yau zuwa gobe za’a basu Cek din.
