Wednesday, June 3
Shadow

An gayawa tauraron Barcelona Messi cewa cin kwallaye daya keyi ba baiwa bane

Tim Sherwood yace nasarorin da Lionel Messi ya samu a wasannin kwallon kafa ba baiwa bace naci ne da kuma kokarin da yake yi yasa ya same su, kuma tsohon manajan Tottenham din yace kwallayen da tauraron barcelonan yake ci ba baiwa bace.

 

Mutane dayawa suna tunanin cewa Messi shine zakaran wasan kwallon kafa na duniya kuma yaci kwallaye guda 627 a wasanni guda 718 daya buga a rayuwar shi.
Dan wasan Argentina ya kafa tarihi a gasar la liga saboda yawanci yana cin kwallo a kowane wasa yayin da yayi nasarar cin kwallaye guda 438 a wasanni guda 474 na la liga.
Duk da haka dai Sherwood yace wannan abun ba zai taba zama baiwa ba kuma shi ya yarda cewa nasarorin Messi saboda kokari ya same su. Ya gayawa DailyMail cewa shi bai yarda cewa akwai wani dan wasan mai baiwa ba kuma Messi koya yayi saboda ba’a haka aka haife shi ba.
Tsohon dan wasan ingilan yace kokari dakuma nacin dan wasa yafi akan ace wai baiwa ne. Kuma yana jin haushi sosai idan yaji masu sharhi suna cewa baiwa ne saboda babu baiwa a wasannin kwallon kafa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *