Wani dansanda, Monday Gabriel ya gurfana a gaban babbar kotun jihar Legas inda ake zarginsa da kashe abokin aikinsa, Sergeant Felix.
Monday ya kashe abokin aikin nasa a ranar 13 ga watan Mayu na shekarar 2020.
Saidai wanda ke zargi ya musanta zargin da ake masa.
Mai shari’a, Sherifat Sonaike ta daga sauraren karar har sai zuwa ranar 26 ga watan October.