fbpx
Thursday, February 25
Shadow

An gurfanar da jami’an Hukumar kiyaye haddura ta kasa bisa zargin karba cin hanci

Hukumar yaki da rashawa da cin hanci da rashawa (ICPC) ta gurfanar da wasu jami’an Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC) biyu, kan zargin karbar kudi daga masu ababen hawa.

A cikin tuhume-tuhume 2 da aka gabatar a gaban Mai Shari’a H. Aprioku na Babbar Kotun Jihar Ribas 11 da ke zaune a Fatakwal, ICPC ta fadawa kotun yadda mutanen biyu, John Asegu da Otom Asueni, suka karbi kudi da yawansu ya kai N3,500 daga masu ababen hawa a matsayin “goro” don basu damar wuce shingen bincikensu a kan babbar hanyar Fatakwal zuwa Ahoada, ko da kuwa ba tare da an tuhume su da wani laifi ba.

An kama wadanda ake zargin a kan aikin ne bayan Hukumar ICPC ta yi musu dirar mikiya sakamakon bayanan sirri.

Hukumar ICPC tace a cikin Caji na No: PHC / 3905ICPC / 19 ta bayyana cewa abubuwan da jami’an suka yi ya sabawa doka, kuma za’a masu hukunci a karkashin sashi na 8, 19, da 26 na Dokar Cin Hanci da Rashawa da sauran laifuka masu alaka da hakan, 2000, kuma idan an same su da laifin za’a yanke masu hukunci ɗaurin shekaru 7 ba tare da zaɓi na tara ba.

Saidai mutanen da ake tuhumar sun musanta zargin laifuka 2 da ake tuhumar su kuma Alkalin kotun ya ba da belin su, amma saboda rashin iya biyan ka’idojin belin, sai aka sake tsare su.

An daga karar zuwa 26 ga Maris, 2021 don fara shari’a.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *