Sunday, May 31
Shadow

An gurfanar da Mijin daya kwararawa matarshi ruwan zafi saboda zargin cin Amana a kotu

Hukumar ‘yansandan jihar Osun ta gurfanar da Akinde Adeniyi gaban kotun Majistre dake garin Ille-Ife ida ake zarginshi da zubawa matarshi ruwan zafi saboda zargin tana cin amanarsa.

 

Mijin dai ya zubawa matar tasa tafasashshen ruwan barkono ne tana kwance wanda hakan ya sa mata jiwuka a jiki, kamar yanda mai kara Inspectir Ona Glory ta bayyanawa kotu.

 

Ta kara da cewa ya yi wannan aika-aika ne a Ranar 14 ga watan Afrilun data gabata inda hakan ya jiwa matarsa Alani Deborah ciwo.

 

Saidai mijin ya musanta laifin da ake zarginsa dashi kuma lauyansa ya bukaci a bayar da belinsa.

 

Mai shari’a Joseph Owolawi ya bayyana cewa, ya bayar da belin mijin kan Naira Dubu 100 da kuma wanda zai tsaya masa me yawan irin wannan kudin. Ya kuma daga shari’ar zuwa 4 ga watan Yuni.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *