fbpx
Thursday, March 4
Shadow

An gurfanar da Salihu Yahaya, Hadimin Gwamna a kotu da yawa matarsa kazafin Zina

Hadimin tsohon gwamnan jihar Adamawa Boni Haruna, watau Salihu Yahya ya shiga hannun jami’an tsaro bayan da yawa tsohuwar matarsa kazafin zina.

 

An gurfanar dashi a gaban Kotu a Yola bisa kiran tsohuwar matar tasa, Maryam Tabah da cewa Mazinaciyace.

 

Matar ta bayyana cewa shekarunsu 19 da aure da mijinta amma bayan da suka rabu sai ya rika yadata a Duniya cewa wai ya kamata tana lalata da wani karamin yarone me suna Adamu Buba Bazza shiyasa ya saketa.

 

Maryam tace mijin nata ya gayawa kawarta, Sa’a Luka cewa saboda cin amana ne ya saketa.

 

Saidai Yahaya yace matar tasa karya take. Amma matar ta dage akan abinda ta fada.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *