Wata Kotun Majistare da ke Ado-Ekiti a ranar Talata, ta ba da umarnin tsare wani saurayi dan shekaru 27, Joseph Olaniyi, a cibiyar gyara da ke Ado-Ekiti kan zargin fyade ga yarinya ’yar shekara 13.
Mai gabatar da kara, Insp Olubu Apata, ya fadawa kotu cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 21 ga watan Nuwamban shekarar 2020 a Ado-Ekiti.
Wanda ake zargin yayiwa yarinyar fyade ne tare da yi mata barazanar kisa idan har ta bayyana, A cewar mai gabatar da kara.
Babban alkalin kotun, Mista Abdulhamid Lawal, ya ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara a gidan yari, har sai kotun ta sake zama.