fbpx
Monday, March 1
Shadow

An Gurfanar Da Wani Tsohon Jami’in ‘Yan Sanda Bisa Laifin Baddakama Da Zambar Miliyan N3.7

Wani tsohon dan sanda, Mohammed Mansur, a ranar Laraba ya bayyana a gaban wata kotun Majistare ta Tinubu kan zargin zamba da hannu cikin damfarar miliyan N3.7.

Mansur, mai shekara 36, ​​wanda ke fuskantar tuhuma guda uku da suka hada da zamba, sata da kuma yin baddakama, ya musanta aikata laifin.
Mai gabatar da kara, ASP Ben Ekundayo, ya fadawa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifukan ne tsakanin 2015 zuwa Oktoba 2020 a yankin Ajegunle na jihar Legas.
Ya ce wanda ake kara ya gudu ya bar rundunar ‘yan sanda ta Najeriya (NPF) a 2013 a matsayin kofur.
An kama shi sanye da kakin ‘yan sanda mai mukamin Sufeto ba tare da izini daga rundunar ba.
Ya yi zargin cewa wanda ake karan ya damfari wani Mista Almustapha Umar-Dodo ta hanyar gamsar da shi cewa shi dan sanda ne kuma yana da wasu babura da zai yi gwanjon a madadin NPF.
Ya ce Mansur ya karbi Naira miliyan 3 da dubu 700 daga Umar-Dodo don taimaka masa ya samu babura, abin da ya kasa samu ko mayar da kudin.
Ekundayo ya ce lokacin da aka kama wanda ake zargin, an gano cewa ya gudu daga rundunar ne a 2013.
Mai gabatar da karar ya ce laifukan sun saba wa sashi na 77, 287 da 314 na dokar manyan laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.
Alkalin kotun, Mr A.A. Paul, ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N500,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
Ya dage sauraron karar har sai ranar 24 ga Maris don ambaton.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *