Wata yarinya ‘yar shekaru 15 a jihar Adamawa ta gurfana a gaban kotu bayan da ta amsa laifinta da ta yi wa wata tsohuwa ‘yar shekara 85 duka har lahira.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin 8 ga watan Afrilu.
Matashiyar mai suna Happy David da ake zargin ta yi amfani da sanda ne, ta kai farmaki gidan matar mai suna Gama Jatau da ke unguwar Tambo a karamar hukumar Girei, inda ta lakada mata duka bisa zargin maita.
An garzaya da mamacin zuwa asibiti a Jabbi Lamba a karamar hukumar Girei inda aka tabbatar da rasuwar ta.
Bayan mutuwar tsohuwar, an gurfanar da yarinyar a gaban kotu inda ta amsa laifinta.
Daga nan ne babban alkalin kotun ya dage zaman kotun zuwa ranar 26 ga Mayu, 2022.