fbpx
Friday, December 2
Shadow

An halaka mutum takwas da ƙona gidaje a Filato

Yan bindiga sun kutsa kauyen Wumat da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato tare da kashe mutum 8 da jikkata wasu da dama.

Mazauna kauye sun shaidawa jaridar Daily Trust a Najeriya cewa ‘yan bindiga sun koma kona gidaje 20.

Adamu Isa wani mazaunin Bokkos, ya ce ‘yan bindigar sun kai musu hari ne da misalin 10 na dare, inda suka harbe mutum 8, akwai kuma mutanen da suka jikkata yanzu haka a asibiti, a cewarsa.

Har yanzu dai ‘yan sanda ba su tabbatar da harin ko fitar da karin haske ba.

Karanta wannan  Gwamnonin jihohi ne suka jefa Najeriya cikin talauci, in ji gwamnatin Tarayya

Sai dai harin na baya-bayanan na zuwa ne kwanaki bakwai bayan ‘yan bindiga sun hallaka mutum 11 da jikkata wasu a kauyen Maikatako a nan Bokkos din.

Kwanaki uku kenan da gwamna Simon Lalong ya tattauna da masu ruwa da tsaki a Bokkos domin samar da mafita kan rikice-rikice da ake samu a karamar hukumar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *