
Babbar kotun Turai ta warware saki irin na Musulunci da wani dan asalin kasar Syria da ke zaune a Jamus ya yi wa matarsa, tana mai cewa shari’ar Musulunci ba ta da gurbi a Tarayyar Turai.
Kotun ta tarayyar Turai ta ce kasashen na Turai ba sa bukatar amincewa da saki irin na Musulunci wanda kotunan ba su san da shi ba.
Wasu Musulmi sun yarda cewa idan mutum ya ambaci saki uku sau daya aurensa da matarsa ya rabu kwata-kwata.
Wannan shi ne karo na farko da aka taba yanke irin wannan hukunci a Turai.
Yaya al’amari ya faru?
Miji da matar sun yi aure ne a birnin Homs na kasar Syria a shekarar 1999 kafin su yi kaura zuwa Jamusy. Yanzu dai suna da takardun zama dan kasa na kasashen biyu.
A shekarar 2013 ne mutumin ya yi wa matar saki uku sau daya a wata kotun Musulinci da ke birnin Latakia na Syria. Sai dai kotun Turai ta ce sakin ya shafi mutumin da matar ne kawai don haka hukumomi ba su amince da shi ba tunda ba su sanar da su ba.
Matar ta karbi takardar sakin nata amma ta ki amincewa da sakin lokacin da tsohon mijin nata ya bukaci wata kotun birnin Munich na Jamus ta tabbatar da sakin.
bbchausa.