A yammacin ranar litinin akayi artabu tsakanin wasu mutanen da ake kyautata zaton dakarun soji ne da hukumar ‘yan sanda a jihar Bayelsa, inda sojojin suka harbi yan sanda guda biyu.
Lamarin ya faru ne a wurin wani shataletale dake babban birnin jihar watau Yanegua, bayan wani soja ya saba dokar titi ya shigo ba’a bashi hannu ba.
Inda suka fara cacar baki da ‘yan sandan har ta kaiga sun mari sojan, amma daga bisani daya nuna masu cewa shi soja ne sai suka bashi hakuri kuma ya wuce.
Amma ya dawo tare da abokansa guda biyu dauke da bindugu suka fara dukan ‘yan sanda da bindugun har suka harbi mutane biyu da bindiga.