fbpx
Friday, June 9
Shadow

An kama ɗan sandan Najeriya saboda nuna goyon baya ga ƙungiyar asiri

Wani kofur ɗin ɗan sanda da ke aiki da rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Jihar Ebonyi ya shiga hannu sakamakon nuna goyon bayansa ga wata ƙungiyar asiri.

An ga Matthew Isaac a wani bidiyo da ya karaɗe intanet yana rawa tare da ɗaga bindigar da ke hannunsa yayin da yake yabon ƙungiyar asirin.

Kakakin ‘Yan Sanda na Ƙasa CSP Muyiwa Adejobi ya faɗa cikin wata sanarwa cewa a yau Lahadi cewa Sufeto Janar Usman Alkali Baba ya yi Allah-wadai da aikin kofur ɗin kuma ya umarci a ɗauki matakin da ya dace.

Karanta wannan  Dalibai a kasar China na biyan Naira Dubu 43,000 a kowanne awa dan a koyar dasu yanda ake murmushi

Sanarwar ta ce “aikin ɗan sandan yunƙuri ne na shafa wa rundunar ‘yan sanda baƙin fenti”.

“Abin da ya aikata ya saɓa wa dokokin amfani da shafukan sada zumunta da sauran dokokin ɗa’ar dukkan ‘yan sanda,” in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *