Hukumar kula da Shari’a ta Kano ta hukunta wasu alkalai a jihar saboda aikata ba daidai ba.
Alkalai uku ne dai da maga takarda a babban kotun jihar aka hukunta ciki hadda alkalin da yayi yunkurin satar kudi daga asusun wanda ake tuhuma.
Kakakin hukumar Baba Jibo-Ibrahim ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Yace wadanda ake zargin sune Magistrate Rabi Abdulkadir, Magistrate Talatu Makama, da Magistrate Tijjani Saleh-Minjibir.
Sanarwar tace an dauki matakin ladabtarwar ne dan tsaftace bangaren shari’a na jihar.