fbpx
Thursday, May 26
Shadow

An kama dan Najeriya a kasar Indiya da hodar Iblis da kwayar Mephedrone na naira miliyan 16.4

Hukumar yan sandan Mumbai dake Indiya sun bayyana cewa sun kama wani dan Najeriya mai suna Olivier Diba Nikki da miyagun kwayoyi na naira miliyan 16.4.

Inda manema labarai na Indiya suka bayyana cewa an kama shi ne a gabashin Mumbai da hodar iblis da kuma kwayar mephedrone.

Kuma hukumar yan sandan sun bayyana cewa sun kwace miyagun kwayoyin daga hannun shi, inda yace masu dama a watan disemba aka sako shi daga hannun hukumar NDPS, wadda ke yaki akan masu halkallar miyagun kwayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.