‘Yan sanda a jihar Nasarawa sun kama Bako Anjeh da yawa wata yarinya me shekaru 17 fyade har sai da ta mutu.
Lamarin ya farune a karamar hukumar Nasarawa-Eggon dake jihar.
Rahoton yace mutumin yayi amfani da maganin kashe ciyawa wajan baiwa yarinyar jikinta ya mutu kamin ya afka mata.
Kakakin ‘yansandan jihar, Ramhan Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna kan bincike.