fbpx
Monday, August 8
Shadow

An kama dansandan Najeriya bayan da ya fasawa Wani matashi kai

Lamarin ya farune a Abraka dake jihar Delta inda ‘yansanda suka shiga gidan wani matashi, Kelvin Ilome dan shekaru 27.

 

Ya nemi su bashi izinin da aka basu na masa bincike a gida amma suka kiya inda suka kamashi aka tafi dashi ofishin ‘yansansan, dansanda, Corporal Godspower ya buga ma amatashin kulki akai wanda hakan ya kai ga fashewar kansa.

 

Dan rajin kare hakkin bil’adama, Harrison Gwamnishu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yake an kama dansandan da yayi wannan aiki amma suna neman a hukuntashi.

Karanta wannan  'Yan bindiga sun kashe insfetoci biyu tare da wani dan Indiya a wani kamfani dake jihar Imo

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.