An kama wani dansandan Najeriya, Ibrahim Odege da wani Samason Odege yayin da suke fashi a Rukunin gidaje na Elekahia dake fatakwal jihar Rivers.
Kakakin yansandan jihar, Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kama wanda ake zarginne da misalin karfe 10 na daren Asabar.
Mazauna wannan rukunin gidaje sun bayyana cewa sune suka kama barayin suka dankasu a hannun yansanda.