Sunday, May 31
Shadow

An kama DPO da ya dirkawa Abokin aikinsa dansanda Harsashi ya mutu a Legas

DPOn ‘yansanda, na yankin Ilemba Hausa, Yahaya Muhammad Adeshina ya shiga hannu bayan Dirkawa abokin aikinsa harsashi bisa kuskure yayin da suke korar mutane daga bakin ofishin nasu.

Harsashi bindigar DPOn ya kashe Sajan Onalaja Onajide, kuma tuni aka kama DPO kuma aka kwace bindigarsa kamar yanda me magana da yawun ‘yansandan jihar Legas, Bala Elkana ya bayyanar.

 

Ya kara da cewa da farko an kama wasu sojoji 2 ne da ake zargi da harbin wanda ake tsammanin sun gudu daga wajan aiki ne amma da gaskiya ta bayyana sai suka kama DPO din.

 

Yace ana ci gaba da bincike akansa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *