fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

An Kama Mai Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kaduna

Rundinar ‘yan sanda reshen jihar Kaduna ta samu nasaran aika wasu miyagun ‘yan ta’adda 4 masu garkuwa da mutane zuwa garin da ba’a dawowa.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kaduna DSP Muhammad Jalige ya shaida wa manema labarai cewa an jima ana bibiyar ‘yan ta’addan, an datse su akan hanyar Saminaka zuwa Jos suna tafiya a cikin mota kirar Sharon blue colour direban motar mai suna James Dawi, dan shekara 31 wanda ya fito daga garin Vom karamar hukumar Jos South jihar Plateau.

Lokacin da ‘yan ta’addan suka lura ‘yan sanda na bin diddiginsu akan hanyar Saminaka zuwa Jos, sai suka bude wa ‘yan sandan wuta, a gurin musayen wuta na tsawon mintuna 30 ‘yan sanda suka samu nasaran aika ‘yan ta’addan zuwa garin da ba’a dawowa.

Karanta wannan  An kama matar data sace diyar makwabtanta

Bayan ‘yan sanda sun duba motar ‘yan ta’addan, sun samu bindigogi kirar AK47 da hardashin bindiga guda 140, sannan ‘yan sanda sun kama wannan matar bafulata da kuke gani a hoto wacce ta ke sana’ar safaran bindigogi da harsashi zuwa ga ‘yan ta’addan jeji a cikin jihar Kaduna.

Allah Ka nuna mana karshen ‘yan ta’adda a Kasarmu Nigeria

Daga Datti Assalafiy

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.