fbpx
Friday, March 31
Shadow

An Kama Malam Bello Yabo, Sokoto

Yanzun nan daya daga cikin manyan Daliban Sheikh Bello Yabo wato Dr MD Shuni yake sanar da ni labarin cewa an kama Malam Bello Yabo, an kai shi jihar Kaduna za a wuce da shi Abuja.

 

 

Jama’ar Musulmi kowa ya kwantar da hankalinsa, idan an ce hukuma ce ta kama ka to abin ya zo da sauki, kowa na hukuma ne, har shugaban Kasa bai fi karfin hukuma ba.

 

Kuma dai duk wanda ya san Malam Bello Yabo ya san da cewa wannan kamu ba sabon abu bane a gurinsa, ya taba yin shekaru 8 a gidan yari saboda fada da miyagun ‘yan siyasa.

 

 

Wannan shine tafarkin ‘yan gwagwarmayar jaddada gaskiya da adalci, duk wani ‘dan gwagwarmaya na gaskiya to sai ya shirya wa kamu da dauri har ma da kisa.

Karanta wannan  HOTUNA: Yadda Jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Ya Harɗe Kafa Yana Yi Wa Zaɓaɓɓun 'Yan Majalisar Jihar Kano Jawabi Bayan Da Suka Karɓi Takardar Shaidar Cin Zaɓen Su A Jiya

 

 

Ina tuna wani lokaci da Sheikh Bello Yabo yake yin zazzafan raddi ga manyan ‘yan Luwadi, yace wallahi bai taba rabe tsakanin gidan yari da dakin matarsa ba, duk daya ne.

 

 

Kuma a yawancin lokuta kamu da dauri a gidan yari yana karawa mutumin da ya tsayu a kan gaskiya girma da daukaka ne, kamar misalin abinda ya faru da Annanin Allah Annabi Yusuf.

 

 

Muna rokon Allah Ya amintar da Malam Bello Yabo daga dukkan sharri, Allak Ka bashi mafita na alheri Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Datti Assalafiy

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *