An kama wani malamin makarantar islamiyya a jihar Legas mai suna Faruq da laifin yin lalata da dakibansa yara guda tara.
Inda alkakin kotun dake amsar karan masu aikata lalata ta jihar Legas ya bayyana cewa malamin ya saba dokar jihar sashe na 261 na shekarar 2015.
Bakwai daga cikin yara ne suka bayyana cewa malamin su na Islamiyya ne yake yin lalata dasu ta hanyar sanya dan yatsarsa a farjinsu.
Kuma sun bayyana hakan ne bayan da iyayensu suka kaisu wurin wata malamar asibiti domin ta duba lafiyar su.