fbpx
Saturday, August 20
Shadow

An kama matar da ta yi yunƙurin ‘sayar da ɗan kishiyarta’ a Zamfara

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Zamfara ta kama wata mata da take zargi da da yunƙurin sayar da yaro ɗan shekara biyu.

Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito kwamishinan ƴan sanda na jihar, Ayuba Elkana inda ya ce an kama matar ne tun a ranar 8 ga watan Janairu a yankin Tullukawa da ke Gusau inda ake zargin matar da yunƙurin sayar da ɗan kishiyarta.

Matar wadda asalinta mutumiyar ƙauyen Danyade ce da ke Maradi a Jamhuriyyar Nijar, an kama ta ne ɗauke da ɗan kishiyarta wadda ta shaida wa jami’an tsaro cewa ta sato yaron ne daga kishiyarta domin ita ma ta rama sata da sayar da ɗanta da kishiyarta ta yi a baya.

Karanta wannan  So makaho ne: Wata matashiya 'yar shekara 15 ta yiwa kanta allurar jinin sahibinta mai dauke da cutar kanjamau

Amma daga baya ta ƙara shaida wa jami’an tsaro cewa ta yi yunƙurin sayar dsa yaron ne domin samun kuɗin biyan buƙatunta na yau da kullum.

Rundunar ƴan sandan ta ce za a miƙa wadda ake zargi zuwa ga hukumar kula da shige da fice ta Najeriya domin zurfafa bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.