Sunday, May 31
Shadow

An kama matar data kashe surukarta ta hanyar caka mata wuka

Hukumar ‘yansandan jihar Naija Sun kama wata mata me suna Fatima Sani wadda ake zargi da kashe surukarta ta hanyar caka mata wuka.

 

Kwamishinan ‘yansandan jihar,Alhaji Adamu Usman ne ya bayyana haka ga manema labarai Ranar Litinin inda yace Fatima me shekaru 37 ta fitone daga kauyen Gobirawa a karamar Hukumar Mashegu dake jihar.

 

Yace sun samu matsalane da mijinta, Sani Umaru a ranar 23 ga watan Afrilu inda hakan yayi sanadin mijin ya saketa.

 

Ita kuwa sai ta zargi cewa mahaifiyar mijin nata, A’ishatu Umar me shekaru 70 ce ta sashi ya saketa dan haka taje har gida ta kasheta da wuka.

 

Yace ana ci gaba da bincike kuma za’a gurfanar da mai laifin a gaban kuliya dan hukuntata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *