Jami’an tsaro sun kama wata mata data sace diyar makwabtanta.
An kama Miss Chinwendu Umegbaka me kimanin shekaru 38 ne da yarinyar me shekaru 3 da niyyar sayar da ita.
Kakakin ‘yansandan jihar Anambra inda lamarin ya faru ya bayyana cewa, bayan kama matar, an mayarwa da iyayen yarinyar diyarsu.
Yace suna ci gaba da bincike kan lamarin.