fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

An kama matashin daya kira abokansa suka lakadawa budurwasa duka a jihar Kwara

Hukumar ‘yan sanda na jihar kwara ta kama wani matashi tare da abokansa guda biyar daya kira suka lakadawa budurwsa duka kan ta yaudare shi.

Inda mai naga da yawun hukumar Okasanmi Ajayi ya bayyana cewa yarinyar tace saurayin nata ya kirata ranar litinin cewa tazo gidansa kuma taje.

Wanda anan ne shi da abokansa suka rike mata hannaye da kafafuwa suka zane ta sukace tana bin samari, amma ta musanta hakan.

A karshe dai tace bataga amfanin kama saurayin nata ba saboda ya rigada ya cuceta kuma ba za’a rama mata abinda ya mata ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.