fbpx
Saturday, August 20
Shadow

An kama matashin dake amfani da sunan Kwamishina yana yaudarar mata yana lalata dasu

‘Yan sanda a jihar Akwa-Ibom sun kama wani matashi dake amfani da suna  kwamishina yana yaudarar mata.

 

Matashin me suna Mr. Imaobang Akpan yayi karyar cewa shi hadimin kwamishinane inda yake cewa zai samarwa matan aikin yi.

 

Yakan kaisu otal daban-daban yayi lalata dasu, saidai da suka ganoshi sun kai karasa, inda kuma aka damkeshi.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Odiki Macdon ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda yace bai san abinda ya kaishi ga aikata wannan aika-aika ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.