fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

An kama matashi, Usman dake amfani da sunan mata yana aikawa maza hotuna Batsa a shafukan sada zumunta

Kotu a Kwara, jihar Ilorin ta daure wani matashi dan shekaru 28, Usman Muhammad bayan samunsa da laifin amfani da sunan mata a shafukan sada zumunta da kuma aikawa maza hotunan batsa suna bashi kudi.

 

Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta EFCC ce ta gurfanar dashi a gaban kuliya inda wakilin hukumar, Adenike Yoku ya bayyana cewa an kama Usman a gidansa, a Abekuta dake jihar Ogun bisa wannan laifi.

 

Usman dai ya amsa laifinsa. Mai shari’a, Sikiru Oyinloye ya yanke masa hukuncin biyan Naira Dubu 50 cikin awanni 24 ko kuma a daureshi tsawon watanni 6.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.