fbpx
Monday, March 1
Shadow

An kama Mutane 3 da suka kutsa cikin fadar Basaraken garin Yarbawa suka lakada masa duka

An kama wani mutum dan shekaru 35, Wasisu Tijani da wasu 2 aka gurfanar dasu a gaban Kotu saboda zuwa fadar Wani Basaraken jihar Osun suka lakada masa duka.

 

Sauran sune Tairu Akande da Samad Mutairu wanda suka shiga fadar Alabudo of Abudo suka lakada masa dukan kawo wuka.

 

Dansanda Me gabatar da Kara, Kayode Asambe ya bayyana cewa, wanda ake zargin sun kuma lakadawa ma’aikata a fadar Sarkin duka, ranar 20 ga watan Fabrairu.

 

Saidai duk sun ki amsa laifinsu. Lauya me karesu, MS. Okgi ya nemi a bada belinsu amma kotun ta ki amincewa inda ta ce a dauresu a gidan yari har zuwa 25 ga watan Fabrairu da za’a ci gaba da shari’a.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *