fbpx
Monday, August 8
Shadow

An kama mutane 4 masu safarar yara a Jihar Gombe

Hukumar ‘yansandan jihar Gombe ta bayyana cewa, ta kamata mutane 4 da ake zargi da safarar yara 12.

 

Kwamishinan ‘yansandan jihar Maikudi Shehu ya bayyana cewa an kama wanda ake zarginne bisa hadin gwiwar ‘yansandan jihar Anambra.

Ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN cewa wanda aka kama din sune Haiwa Usman, me shekaru 37 daga jihar Gombe sai Nkechi Odulanye, me shekaru 54 daga jihar Anambra, Faith Okpi, me shekaru 38 itama daga jihar Anambra sai Bala Shaukali daga jihar Taraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.