fbpx
Saturday, September 23
Shadow

An kama mutane uku da laifin fyade da tilastawa wata yarinya ‘yar shekara 15 shiga kungiyar asiri

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar 30 ga watan Yuni ta kama wasu mambobin kungiyar asiri ta Eiye confraternity guda uku, wadanda suka shigar da wata yarinya da karfi cikin kungiyarsu bayan sun yi mata fyade.

Wata sanarwa da DSP Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya fitar, ta ce wadanda ake zargin, Daniel Njoku a.k.a Agege, Damilare Ogundiran, da Adebayo Olamilekan, an kama su ne biyo bayan rahoton da mahaifiyar yarinyar ta kai a hedikwatar sashin Ajuwon, wadda ta ruwaito cewa ta aiki ‘yarta ‘yar shekara 15 zuwa wani waje a unguwar Akute Odo, amma Daniel Njoku ya tare mata hanya, inda ya kai ta da karfi wajen ‘yan kungiyarsa a maboyarsu inda aka yi wa yarinyar fyade tare da yi mata dukan tsiya da karfi da kuma tilasta mata shiga Eiye cult group.

Mai karar ta kuma bayyana cewa wadanda ake zargin sun yi wa diyarta barazanar cewa za a kashe ta idan ta sanar da kowa lamarin.

Wadanda ake zargin sun amsa laifin da suka aikata, sun sanar da ‘yan sanda cewa suna matukar neman karin ‘ya’yan kungiyar da za su shiga kungiyarsu musamman mata, kuma hakan ne ya sa suka yi abin da suka yi.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wadanda ake zargin zuwa sashin yaki da ‘yan kungiyar asiri na sashen binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *