fbpx
Sunday, February 28
Shadow

An kama mutum fiye da 100 a Kano kan ƙin bin dokokin korona

Gwamnatin Jihar Kano ta kama kusan mutum 150 bisa laifin karya dokokin kariya daga annobar cutar korona.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a yau Litinin.

Ya ƙara da cewa dakarun tabbatar da bin dokar korona da kuma sauran jami’an tsaro za su ci gaba da tilasta bin dokokin.

Sanarwar ta ce an ci tarar mutum 102 naira 5,000 kowannensu, yayin da kotu ta musamman ta tsare mutum 25 a gidan gyara hali.

A makon da ya gabata ne Alƙalin Alƙalan jihar ya rantsar da kotuna guda 21 na tafi-da-gidanka domin hukunta masu karya dokar daƙile yaɗuwar cutar ta korona a jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *