Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi reshen jihar Sokoto, NDLEA ta kama shugaban wani kauye da kuma mutane 10 bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.
An kama shugaban kauyen Gidan Abba dake karamar hukumar Bodinga ta jihar ta Sokoto me suna Abubakar Ibrahim tare wasu 10.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Baba Femi ya sanar da haka.
Yace hukumar tasu ta kuma yi nasarar kama mutane a Kogi, Abuja, Da sauran wasu jihohi.
Hakanan kuma ta kama kwayoyi da aka shigo dasu Najariya daga wasu kasashen ketare.