Sunday, May 31
Shadow

An kama uban da ya shafe shekaru 8 yana lalata da diyarsa

Jami’an ‘yansanda a jihar Legas sun kama Ede Tyndale me shekaru 50 da zargin shafe shekaru 8 yana wa diyar cikinsa fyade.

 

Mahaifiyar yarinyar ce ta hano haka bayan data ga irin rainin da diyar tawa mahaifinta.

 

Tace ta dake ta ba sau daya ba ba sau biyu ba akan rainin da yarinyar tawa mahaifinta, kuma ta mata fada amma a banza, tace daga baya data ga dukan ba zai yi ba shine ta koma mata nasiha. A hakane take bata labarin abinda ke faruwa.

 

Yarinyar ta bayyana cewa tun tana da shekaru 11 mahaifinta ke mata fyade, idan ta kiya sai yace zai daketa ko kuma ya kashe ta idan ta sake ta gayawa wani. Dalilin da yasa kenan ita kuma take ganin watakila idan tana mai rashin kunya zai kyaleta.

 

Me magana da yawun ‘yansandan Legas, DSP Bala Elkana ya bayyanawa Vanguard cewa sun kama mahaifin kuma ya amsa laifinsa.

 

Ya kara da cewa tuni suka gurfanar dashi a gaban kotun Magistrate dake Ogba dan hukuntashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *