Wani matashi, Afeez Olalere ya kashe kaninsa saboda yin tsafi ya samu kudi, abinda ake cewa, Yahoo Yahoo.
Ko da aka kama dan shekaru 32 din, ya bayyana cewa da sanin mahaifiyarsa ya aikata abinda ya aikata.
Yace mahaifiyarsa ce ta kaishi wajan boka inda bokan ya gaya masa cewa, idan yana son kudi, sai ya kashe wani dan uwansa.
Yace bokan yace su kai masa sassan jikin dan uwan nasa, yace da suka koma gida, sai mahaifiyarsa ta bashi guba ya baiwa kanin nasa ya sha ya mutu kuma suka yanki sassan jikin da zasu kaiwa bokan.
Asirinsu ya totune yayin da suke shirin kai gawarsa makabarta.