(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Rundunar ‘yan sandan kasar ta ce mutum ukun da take tsare da su sun tabbatar da hannunsu a harin da aka kai wa basaraken.
Sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na Twitter ta ce mutanen na da hannu a ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane a sassan arewacin kasar kuma suna bai wa ‘yan sanda muhimman bayanai.
Kakakin ‘yan sandan kasar Frank Mba ya ce rundunar na bincike domin dakile aiyukan kungiyar da sauran bata gari.
Da yake kira ga jama’a da su nuna kishin kasa ta hanyar bayar da bayanai kan bata gari, Frank Mba ya koka bisa yadda wasu ‘yan kasar ke rufa wa miyagu asiri.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole