fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

An kama wanda suka kashe yarinyar da suka yi garkuwa da ita bayan karbar kudin fansa Dubu 150 a Bauchi

Jami’an hukumar tsaro ta Civil Defence a Jihar Bauchi sun kama wasu maza biyu bisa zargin yin garkuwa da kashe wata yarinya ‘yar shekara biyar bayan karbar kudin fansa a hannun iyayenta.

Yayin gabatar da wadanda ake zargin gaban manema labarai a hedikwatar NSCDC da ke Bauchi a ranar Litinin, kwamandan jihar, Nuruddeen Abdullahi, ya ce mutanen sun yi garkuwa da yarinyar ne a kofar gidansu, inda suka tafi da ita karkashin wata gada suka shake ta suka saka ta cikin buhu duk da cewa sun karbi kudin fansa a wajen iyayenta.

Karanta wannan  HASASHE: Mai yuwuwa Osinbajo ya kauracewa zuwa Sokoto ganawa da delegate saboda bacin ran ki$an Debor@h

Rahotanni sun ce daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da yarinyar makwabcinsu ne.

Yarinyar mai suna Khadija, makwabcin nasu ya sace tane a lokacin da take wasa a kofar gida, inda da farko ya nemi a bashi kudin fansa naira miliyan daya, amma daga bisani aka tsaya a kan naira dubu 150.

Lamarin dai ya faru ne a garin Na Rabi, da ke Bauchi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.