Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Oyo ta cafke wani fasto a cocin Cherubim da Seraphim, Mista Jimo Odunayo, mai shekaru 72 bisa zargin yin lalata da yarinya‘ yar shekara 13.
Yan sanda sun kuma cafke Opeyemi Rasaq wanda ya taka rawa a cikin laifin da faston ya aikata tsakanin shekarar 2019 da Yunin 2020.
Kwamishinan ‘yan sanda ta jihar Oyo, Ngozi Onadeko wanda ta gabatar da wadanda ake zargin tace;
“Wanda ake zargin da iyayen yarinyar suna zaune ne a cikin gida guda, kuma yarinya da abin ya shafa a ko da yaushe tana zuwa dakin wanda ake zargin don kallon talabijin, sakamakon haka, wanda ake zargin ya yi amfani da wannan damar wajen yin lalata da ita ta hanyar da ba ta dace ba.”
Bayan cikakken bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin kuma an gurfanar da shi a gaban kotu.