fbpx
Monday, March 1
Shadow

An kama wani fasto saboda yin luwadi da wani yaro dan shekara 12 a Jihar Akwa Ibom

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Akwa Ibom ta cafke wani fasto dan shekara 31, mai suna Anietie Inyang a kauyen Ikot Ebak, karamar hukumar Essien Udim da ke jihar, bisa zargin yin lalata da wani karamin yaro dan shekara 12.

Ana zargin fasto Anietie Inyang da yin luwadi da yaron, wanda ke zaune tare da kaka yaron a Ikot Ada Utor da ke Afaha Clan kuma a karamar hukumar Essien Udim.

A cewar Sitippe, tun da farko rundunar ‘yan sanda ta Essien Udim ta cafke wanda ake zargin amma an ba da belinsa ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba kuma an yi kokarin rufe lamarin.

Amma matar Shugaban karamar hukumar Essien Udim, Misis Umoh Gabriel Tony Luke tare da mijinta, Anthony Luke sun samu labarin kuma sun umarci ‘yan sanda da su gabatar da wanda ake zargin.

An kuma sake damke shi tare da tsare shi a hedikwatar ‘yan sandan jihar a Ikot Akpan Abia, Uyo.

A halin yanzu hukumar dake kula da takaita rikici ta Jihar ce dauki nauyin lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *