fbpx
Sunday, February 28
Shadow

An kama wani magidanci da yake kokarin rubuta wa matarsa ​​jarabawa a lokacin daukar Malamai a Jihar Osun

An kama mutumin mai suna, Adekunle Aremu a lokacin da yake kokarin rubuta wa matarsa, Oyinade Sade Adegbite jarabawar daukar aikin koyarwa a cibiyar CBT ta kwalejin Ilesha dake Jihar Osun.

Jami’ar yada labarai a Ma’aikatar Ilimi, Roseline Olwawuni, ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Laraba 10 ga watan Fabrairu, ta ce an kama wanda ake zargin tare da taimakon jami’an tsaro na Civil Defense.

Ta kara da cewa an kama shi ne bayan anga hoton fasfo dinsa bai yi daidai da hoton da aka ajiye da bayan matarsa ba a cikin na’ura mai aiki da kwakwalwa.

Dangane da lamarin, Kwamishinan Ilimi ta Jihar, Hon. Folorunsho Oladoyin ta yi Allah wadai da wannan dabi’ar ta zamba, tana mai jaddada cewa abin kunya ne a samu wani da yake son zama malami da aikata irin wadannan dabi’u.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *