fbpx
Thursday, May 26
Shadow

An kama wani mai fataucin yara a lokacin da yake kokarin samar da fasfo ga wata yarinya mai karancin shekaru zuwa Dubai

Jami’an hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) reshen jihar Anambra tare da hadin gwiwar hukumar shige da fice ta kasa reshen jihar Anambra, a ranar Laraba 11 ga watan Mayu, sun kama wani da ake zargi da safarar yara kanana tare da ceto wata karamar yarinya da yake kokarin zuwa da ita a kasar Dubai.

Wanda ake zargin wanda ke zaune a Onitsha, tare da hadin gwiwar ‘yan kungiyarsa dake jihar Edo da kuma Dubai, ya dauki yarinyar daga jihar Edo zuwa jihar Anambra.

Karanta wannan  Yan sanda sun kama wasu da ake zargin ‘yan fashi ne a Bayelsa, sun kwato bindigogi

An kama wanda ake zargin ne a ofishin shige da fice a lokacin da yake kokarin samo fasfo na Najeriya domin ya fita da yarinyar zuwa Dubai. A halin da ake ciki, hukumar ta NAPTIP ta kai yarinya zuwa wani gida mai tsaro yayin da ake ci gaba da bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.