fbpx
Wednesday, March 29
Shadow

An kama wani matashi kan kisan maigida a jihar Edo

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta cafke wani yaro dan shekara 17 mai suna Chukwuebuka Nwode bisa zargin kashe ubangidansa, Peter Onoberhie.

An kama Nwode ne tare da wasu ‘yan ta’adda biyu a lokacin da suke kokarin siyar da motar maigidan nasa a Kasuwar Motoci ta Uwelu, da ke garin Benin.

An ce wanda ake zargin yana daya daga cikin ma’aikatan kamfanin samar da ruwa na buhu mallakin mamacin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Edo, Kontongs Bello wanda ya zanta da manema labarai a lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin tare da wasu mutane 11 da aka kama da laifuka daban-daban, ya tabbatar da cewa yaron dan shekara 17 ya kashe wanda aka kashe tare da hada baki da wasu mutane biyu don sace motarsa.

Karanta wannan  Yan fashi sun fasa kabarin wani zabaya don sace sassan jikin gawarsa

Da yake amsa laifin, Nwode ya ce ya yi amfani da wukar dakin girki wajen kashe ubangidansa a lokacin da yake kallon talabijin da tsakar dare a dakinsa.

Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *