Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani matashi mai suna Sakiru Famuyiwa mai matsakaicin shekaru a ranar Juma’a 15 ga watan Afrilu a unguwar Ijeja da ke Abeokuta bisa laifin satar yara biyu a wata coci.
An kama wanda ake zargin ne biyo bayan kiran da jami’an ‘yan sanda suka samu a hedkwatar sashen Ibara cewa, a yayin da ake gudanar da hidimar Good Friday a cocin celestial Church na Christ Ijeja, wanda ake zargin da wani wanda a halin yanzu ke hannunsu, suka kutsa cikin sashen kula da yara inda suka yi awon gaba da yara 2 masu shekaru biyu da uku.
A kan hanyarsu ta fita tare da yaran da aka sace, wani dan cocin da ya gansu ya hango su, ya kuma sanar da jama’ar gurin, sakamakon haka ’yan mutane suka bi su suka kama daya daga cikinsu.
Da wannan kiran na bakin ciki, DPO reshen Ibara, CSP Nasirudeen Oyedele, ya yi gaggawar tura mutanensa, inda suka nufi wurin da lamarin ya faru inda aka ceto wanda ake zargin daga fusatattun mutane da ke shirin kashe shi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar wa manema labarai haka, ya ce kwamishinan ‘yan sandan, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin cikin gaggawa ga sashin yaki da masu garkuwa da mutane na sashen binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da shi a gaba kuliya.