fbpx
Wednesday, March 3
Shadow

An kama wani mutum da ake zargi da dabawa matarsa wuka har lahira kan zargin cin amana a Jihar Ogun

Jami’an rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ogun sun cafke Sobola Olatunji dan shekaru 46 kuma ma’aikacin karamar hukumar Remo ta Arewa da ake zargi da dabawa tsohuwarsa 38y wuka har lahira kan zargin tana mu’amala da wasu maza a Waje.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya tabbatar faruwar lamarin ga manema labarai, ya ce an cafke wanda ake zargin ne bayan wani korafi da mahaifin marigayiyar, Alhaji Ambali Yinusa, ya gabatar a gaban ofishin hedkwatar Owode-Egba cewa surukinsa Sobola Olatunji ya samu rashin jituwa da matar sa, Momudat Sobola, wanda hakan ya haifar masu da fada buga in buga a tsakanin su.

Ya kara da cewa, suna cikin dan sai, Sobola Olatunji ya dauki wuka ya daba wa matar tasa a baya.

Bayan rahoton, DPO Owode-Egba, Csp Matthew Ediae ya aike da masu bincikensa zuwa wurin inda aka kama wanda ake zargin ba tare da bata lokaci ba kuma aka hanzarta da matar zuwa asibiti don bata agajin gaggawa, amma yayin da likitocin ke Kokari ceto rayuwar ta, sai rai yayi halinsa.

Wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ya auri marigayiyar na tsawon shekaru 20, ya na zargin matar sa da yin mu’amala da wasu maza a wajje saboda wasu sakonnin tes da ya gani a wayar ta, wanda hakan ne yasa sukayi rikicin da yayi sanadiyyar mutuwar ta.

A halin yanzu yana hannun jami’an tsaro domin cigaba da bincike kafin a tura fayil din zuwa kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *