Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta kama wani matashi mai matsakaicin shekaru mai suna Collins Edahbor, bisa zargin yin lalata da wata ‘yar aikin gida ‘yar shekara 11 a garin Benin, babban birnin jihar.
A cewar mazauna yankin, yarinyar da aka shigo da ita daga jihar Binuwai, tana kan hanyarta ne ta dibar ma ubangidanta ruwa, inda aka ce ya yi mata kwanton bauna, inda aka ce ya shigar da ita cikin motar bas ya yi mata fyade kuma ya bar ta jina-jina.
An ce an kai yarinyar wajen wani likita mai zaman kansa wanda ya yi mata dinka ga al’aurarta.
Da yake tabbatar da kamun, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Kontongs Bello, ya ce rundunar tana gudanar da bincike a kan lamarin, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a kan haka a karshen binciken