An kama wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da laifin kashe wata matar makwabcinsa da diyarta mai shekaru 4 a jihar Kebbi.
LIB ta ruwaito cewa an tsinci gawar Sadiya Idris mai shekaru 25 da diyarta Khadija a gidansu dake titin Labana, Sani Abacha Bye pass, Birnin Kebbi a ranar 11 ga watan Afrilu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar yayin da yake gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Birnin Kebbi a ranar Laraba 20 ga watan Afrilu, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
Wanda ake zargin ya bayyana cewa ya kashe matar ne bayan ta kira shi da banza, dabba a lokacin da suke cacar baki. Kuma ya kara da cewa ya kashe diyarta ne saboda kada ta tona masa asiri.
Kakakin yan sandan ya kara da cewa, za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike.